banner
News center
Well-rounded experience in hospitality industry.

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Jul 05, 2023

Dakarun sojin Najeriya, da ƴan sanda da kuma sauran jami'an tsaro sun kai samame maɓoyar ƴan a-waren IPOB da ke dajin Orsomoghu da ya haɗa jihohin Anambra da Imo.

Kakakin rundunar, Birgediya-Janar Onyeama Nwachukwu ya ce sun kai samamen ne bayan samun bayanai kan laifukan da ƴaƴan ƙungiyar ke aikatawa wajen tilasta zaman gida na mako biyu a Onitsha da Nnewi da kuma Iheme Obosi da ke jihar Anambra da kuma sabuwar kasuwar jihar Enugu.

Ya ce dakarun sun rusa sansanin ƙungiyar IPOB a Ekeututu da Orsomoghu da kuma Lilu inda suka kama biyar daga cikin ƴan ƙungiyar, tare da ƙwato kayayyaki da dama.

Sojoji biyar da ƴan sanda biyu sun samu rauni saboda abin fashewar da ƴan IPOB ɗin suka tayar.

Rundunar sojin Najeriyar ta ƙarfafa gwiwar jama'ar kudu maso gabashin ƙasar su ci gaba da bai wa jami'an tsaro bayanan da ya dace, su kuma yi watsi da umarnin zaman gida na mako biyu da IPOB ta basu.