banner
News center
Well-rounded experience in hospitality industry.

Me sojojin mulkin Nijar ke nema daga ƙawayensu?

Dec 27, 2023

Asalin hoton, Chadian Presidency

Chadi ce ƙasa ta farko da Mahaman Lamine Zeine ya ziyarta bayan sojoji sun naɗa shi a matsayin firaministan Nijar

Sojojin da ke mulkin Nijar na ci gaba da neman goyon bayan ƙasashe musamman waɗanda ba su nuna adawa da juyin mulkin da suka yi ba a yankin Afirka ta Yamma.

A ranar Talata firaministan Nijar da sojoji suka naɗa, Ali Mahaman Lamine Zeine, tare da wasu mambobin majalisar mulkin soja biyu suka ziyarci Chadi domin tattaunawa da shugaban kasar, Janar Mahamat Idriss Deby.

Zeine - wanda ya je a matsayin fuskar diflomasiyya ta gwamnatin soja - ya ce a yanzu ƙasarsa na ƙarƙashin gwamnatin mulkin soji, yana mai cewa a shirye suke da su buɗe ƙofar tattaunawa.

Kazalika, sojojin mulkin sun tura wata tawaga zuwa Guinea ranar Asabar da ta gabata, duka dai da zimmar neman goyon baya.

Kafin haka, sabon ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Mody, ya je Mali a ranar Juma'a cikin wata gajeriyar ziyara.

Ƙasashen Mali da Burkina Faso da Gueinea mambobin Ecowas ne - ƙungiyar da ke raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma - amma ta takadar da su sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen.

Haka nan dukkansu sun ci alwashin goya wa Nijar baya idan dakarun Ecowas ko na wata ƙasar waje suka kai wa sojojin hari.

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of podcast promotion

A ƙarshen makon da ya gabata gwamnatin sojan Mali ta sanar cewa za ta aika wa Nijar nau'in kayan abinci na hatsi kamar dawa masara da gero saboda takunkumin Ecowas da ya hana sayar mata da kayayyaki.

Chadi ba ta cikin ƙungiyar Ecowas, sannan kuma ba ta nuna adawa ƙarara da juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi ba, amma ta bayyana a fili cewa ba za ta goyi bayan yin amfani da ƙarfi a kan maƙwabciyar tata ba.

Har yanzu Ecowas na ci gaba da yunƙurin difilomasiyya don sasanta rikicin siyasar, duk da barazanar amfani da ƙarfin soja don taka wa sojojin ƙarƙashin Janar Abdourahmane Tchiani birki.

A ranar Alhamis da Juma'a hafsoshin tsaron ƙungiyar za su yi taro a birnin Accra na Ghana don ci gaba da tattaunawa bayan shugabannin Ecowas ɗin sun ba su umarnin ɗaura ɗamarar kutsawa Nijar a makon da ya gabata.

A gefe guda kuma, fitattun mutane da ƙungiyoyi a Najeriya na ci gaba da nuna adawa da yin amfani da ƙarfin yayin da Shugaba Bola Tinubu, a matsayinsa na shugaban Ecowas, yake jagorantar yunƙurin.

Asalin hoton, Chadian Presidency

Mahaman Lamine Zeine ya ce sun tattauna batun sasantawa da Ecowas tare daShugaban Chadi Mahamat Idriss Deby

Cikin wata sanarwa da aka fitar bayan kammala ganawar da ya yi da Shugaban Chadi Mahamat Deby, Firaminista Zeine ya ce "ya je da arzikin maƙwabtaka ne da kuma ƙawance" daga shugaban mulkin sojan Nijar.

"Muna yunƙurin aiwatar da sauyi ne, mun tattauna kan abubuwa sosai da kuma aniyarmu ta tattaunawa da dukkan ɓangarori, amma mun jaddada batun 'yancin ƙasarmu," in ji shi.

Sai dai ya ce gwamnatin mulkin sojan za ta yi magana ne kawai da "ƙawayenta" wadanda ke mutunta 'yancin Nijar a matsayin ƙasa.

Shugaban na Chadi, wanda ke da tasiri da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel, ya yi ƙoƙarin shiga tsakanin sojojin na Nijar da Shugaba Mohamed Bazoum, inda ya gana da ɓangarorin kwana huɗu bayan kifar da gwamnatinsa.

A ranakun Alhamis da Juma'a ne, manyan hafsoshin sojojin kasashen yammacin Afirka (Ecowas) za su gana a birnin Accra na kasar Ghana, domin tattauna halin da ake ciki a Nijar.

Kafin naɗa shi firaminista Nijar, Mahaman Zeine yana aiki ne da Bankin Raya Ƙasashen Afirka a Chadi a matsayin wakilin Nijar. Kazalika tsohon minsitan tattalin arziki ne a gwamnatin Tandja Mamadou, wadda sojoji suka kifar a 2010.

Wannan ta sa wasu masana ke ganin ziyarar da ya kai Chadi na da muhimmanci saboda alaƙar da ke tsakaninsa da mahukuntan ƙasar.

Mahamat Deby ne shugaban wata ƙasa na farko da ya fara ganawa da Mohamed Bazoum da kuma Janar Tchiani bayan juyin mulki lokacin da ya kai musu saƙon matsayar Ecowas da ta cimma a Abuja ranar 28 ga watan Yuli.

"Za a bi ta hannun Chadi ne don a buɗe tattaunawa tsakanin Nijar da Ecowas," a cewar Nasiru Saidu, wani mai sharhi kuma shugaban ƙungiyar Muryar Talaka a Nijar.

"Ke nan ta inda aka hau ta nan za a sauka. A ganina shi ne dalilin kai wannan ziyara, saboda shi [Mahamat] ne ya fara zuwa shiga tsakani," kamar yadda ya bayyana.

Ya ƙara da cewa dole ne Nijar ta nemi hanyoyin rage wa kanta raɗaɗin takunkuman tattalin arziki da Ecowas ta saka mata ta hanyar ƙarfafa alaƙa da ƙawayen nata.

"Dole ne shi firaminista, a matsayinsa na wanda zai jagoranci ministoci da siyasar ƙasa, ya fita ya ƙulla alaƙa da sauran ƙasashen duniya," in ji shi.

"Babu wata ƙasa da za ta iya rayuwa ita kaɗai a fannin tattalin arziki da diflomasiyya da siyasa ba tare da ta yi ƙawance da wasu ƙasashe ba don inganta rayuwar 'yan ƙasarta."

A cewrsa, shi kuma ministan tsaro da ya kai ziyara Mali, ya yi hakan ne don kyautata tsaron ƙasa saboda ƙasashen biyu na da matsala iri ɗaya.

"Dole ya inganta tsaro ta hanyar haɗa kai da Mali da Burkina Faso saboda ta'addancin da ya dame mu. Matsalarmu ɗaya da su."

'Yan bindiga masu iƙirarin jihadi na ci gaba da kai hare-hare a kan iyakar Nijar da Burkina Faso, inda ranar Talata ma aka kashe sojojin Nijar ɗin kusan 17, kamar yadda sanawar gwamnati ta bayyana.

Kafin wannan

Bayani kan maƙalaKorona: Ina Mafita?